West Ham ta dauki Song da Moses da Jelavic

Image caption West Ham tana mataki na takwas a kan teburin Premier da maki shida

West Ham ta dauki dan kwallon Barcelona Alex Song da Victor Moses na Chelsea da dan wasan Hull City Nikica Jelavic.

Kungiyar ta sayi Jelavic kan kudi £3m, yayin da Song da kuma Moses za su buga mata wasanni aro zuwa karshen kakar bana.

Jelavic dan kwallon Croatia ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu, da kuma cewar za a iya kara masa kwantiragi shekara daya idan ya taka rawar gani.

Song dan wasan Kamaru, mai shekaru 27, ya buga wa West Ham wasanni 31 a kakar bara.

Shi kuwa Moses mai shekaru 24, ya sabunta kwantiraginsa da Chelsea zuwa shekaru hudu, sannan ya amince ya buga wa West Ham din tamaula a bana aro.