Kano Pillars ta ci Kwara daya da nema

Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Saakamakon wasannin makwo na 27 da aka buga a gasar Premier Nigeria

Kano Pillars ta samu nasara a kan Kwara United da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan makwo na 27 da suka yi a ranar Laraba.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi Enyimba ta zazzaga wa Ifeanyiubah kwallaye hudu da nema, yayin da Sunshine Stars da Sharks suka tashi wasa canjaras.

Rangers kuwa doke Wikki Tourist ta yi da ci 2-0, Akwa da El Kanemi Warriros suka tashi kunnen doki sai Abia Warriors da ta ci Nasarawa United daya mai ban haushi.

Ga sakamakon wasannin makwo na 27 da aka yi:

  • FC Taraba 2-0 Sharks
  • Enyimba 4-0 FC Ifeanyiubah
  • Bayelsa Utd 1-1Giwa FC
  • Lobi Stars 1-0 Dolphins
  • Akwa Utd 1-1 El-Kanemi
  • Rangers 2-0 Wikki
  • Warri Wolves 4-0 Shooting Stars
  • Abia Warriors 1-0 Nasarawa Utd
  • Kano Pillars 1-0 Kwara Utd
  • Sunshine Stars 0-0 Heartland