FIFA: Wales ta wuce Ingila

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin kungiyar kwallon kafa ta Wales Chris Coleman

A karon farko Wales ita ce ke gaban Ingila a fagen kwallon kafa a matsayin da hukumar kwallon kafa ta duniya watau FIFA ta ke fitarwa a kowane wata.

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Wales Chris Coleman ya ce matsayin zai karfafa gwiwar yan wasansa a karawar da za su yi da Cyprus a ranar Alhamis a wasan neman cancantar shiga cikin gasar EURO da za a yi a shekara mai zuwa.

A cikin jerin sunayen da hukumar ta FIFA ta fitar kasar Argentina ita ce ta daya , Belguim ita ce ya biyu yayin da Jamus ta ke ta uku.

Sauran sun hada da Brazil wadda ta ke ta biyar, da kuma Ingila wadda ta zama ta goma.

A nahiyar Afrika kuwa kasar Algeria ita ce ta daya, kasar Cote d' iVoire tana ta biyu , sai kasar Ghana ta uku yayin da Najeriya ta ke ta tara