Tsohon dan wasan Ghana C.K Gyamfi ya rasu

Image caption Mariyagin lokacin da ya ke taka leda

Tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Ghana wanda ya koma koci C.K. Gyamfi ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.

Gyamfi shi ne dan wasan Afrika na farko da ya taka leda a kasar Jamus, lokacin da ya koma kungiyar kwallon kafa ta Fortuna Dusseldorf a shekara ta 1990 kuma ya taba rike mukamin kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Black stars ta kasar Ghana.

Da yake kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Ghana kuwa marigayin ya dauki kofi har sau uku a gasar kwallon kafa ta Afrika a shekarar 1963 da 1965 da kuma 1982.

Nasarorin da ya yi sun sa ya kasance kocin kungiyar kwallon kafa na Afrika da ya yi fice.

sai dai daga bisani kocin kungiyar kwallon kafa ta Masar Hassan Shehata ya yi nasarar daukar kofi har sau uku a gasar kwallon kafa ta kasashen Afrika da aka yi a shekara ta 2010.