Harry Kane ya nemi shawarar Rooney

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kane ya nemi shawarar Rooney

Dan wasan gaba na kulob din Tottenham, Harry Kane ya nemi shawarar abokin wasansa Wayne Rooney bayan da ya kasa zura kwallo a kakar wasa ta bana.

Kane ya ce "Ina lura da yadda yake gudanar da al'amuransa. Wayne ya yi ba sau daya ba sau biyu ba".

Kane mai shekaru 22, shi ne dan wasa na biyu mafi yawan zura kwallaye a kakar wasa ta 2014 zuwa 2015.

Harry ya zura kwallaye har 21 a lokacin gasar Premier a shekaru biyun.

To sai dai kuma a wannan karon bai iya zura ko da kwallo daya ba.

Harry Kane da Rooney dai sun buga wa Ingila wasanni har guda biyu tare a wasannin neman cancantar buga gasar kwallon kafa ta Turai a shekarar 2016.

Rooney mai shekaru 29, ya ci wa Ingila kwallaye 48 kuma saura kwallo daya tilo da Sir Bobby Charlton wanda ya ciyo wa Ingilar kwallaye 49.