An yi wa Danny Welbeck aiki a gwiwa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Danny ba zai buga wasanni ba na wasu 'yan watanni

Dan wasan Arsenal, Danny Welbeck ba zai buga wasanni ba na 'yan watanni saboda aiki da aka yi masa a gwiwarsa.

Welbeck mai shekaru 24 dai ya sami rauni a kafarsa ne a karshen watan Aprilu bayan da ya zura kwallaye 8 a lokacin wasanninsa guda 32 na farko a kulob din na Arsenal.

Wata sanarwa ta ce " an yanke kudurin yi masa tiyatar ne a makon da ya gabata bayan da aka gano cewa raunin bai warke ba duk kuwa da kulawa ta musamman da aka ba shi".

Wannan dai yana zuwa ne a dai-dai lokacin da kungiyar magoya bayan kulob din na Arsenal suka yi kira da a yi bincike dangane da yadda kulob din ya aiwatar da tsarinsa na musayar 'yan wasa.

Dan wasa daya tal watau Petr Cech kulob din ya saya a kakar wasa ta bana.