Taurarin 'yan Afrika a gasar Premier

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yaya Toure na haskakawa a City

Idan har wasanni farko na kakar wasannin Premier din nan abun da za a yi tunkaho ne, to ya kamata a yaba wa 'yan Afrika wadanda suke taka leda a wasannin Premier na Ingila.

'Yan wasan 'yan asalin Afirka sun zura kwallaye tara a cikin kwallaye 30 a karshen makon da aka fara gasar.

'Yan wasa irin su Yaya Toure na Ivory Coast da Andre Ayew na Ghana da kuma Pappis Cisse na Senegal dukkannin su sun ciri tuta.

'Yan wasa daga nahiyar Afirka guda 45 ne suke barje gumi a gasar Premier ta bana,kuma nahiyar tana da wakilci a kulob 17 daga cikin kungiyoyin wasa 20.

Hakan kuwa na nuna irin karin da aka samu daga 37 a kakar gasar Premier din ta 2014 zuwa 2015.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ayew ya bar Faransa ya taho gasar Premier

Sabbin 'yan Afrika a Ingila:

 • Andrew Ayew: Daga Marseille zuwa Swansea
 • Baba Rahman: Daga Augsburg zuwa Chelsea
 • Papy Djilobodji: Daga Nantes zuwa Chelsea
 • Diermerci Mbokani: Daga Dynamo Kyiv zuwa Norwich
 • Chancel Mbemba: Daga Anderlecht zuwa Newscastle
 • Max Gradel: Daga Saint-Etienne zuwa Bournemouth

Yawan 'yan Afrika a kungiyoyi:

Crystal Place 5

 • Yannick Bolasie (Jamhuriyar Demokradiyyar Congo)
 • Pape Souare (Senegal)
 • Marouane Chamakh (Morocco)
 • Kwesi Appiah (Ghana)
 • Bakary Sako (Mali)

Chelsea 4:

 • John Obi Mikel (Nigeria)
 • Bertrand Traore (Burkina Faso)
 • Baba Rahman (Ghana)
 • Papy Djilobodji (Senegal)

West Ham 4:

 • Cheikhou Kouyate (Senegal)
 • Diafra Sakho (Senegal)
 • Victor Moses (Nigeria)
 • Alex Song (Kamaru)

Newcastle United 3:

 • Papiss Cisse (Senegal)
 • Cheick Tiote (Ivory Coast)
 • Chancel Mbemba (Jamhuriyar Demokradiyyar Congo)

Norwich City 3:

 • Sebastien Bassong (Kamaru)
 • Youssouf Mulumbu (Jamhuriyar Demokradiyyar Congo)
 • Dieumerci Mbokani (Jamhuriyar Demokradiyyar Congo)

Watford 3:

 • Adlene Guedioura (Algeria)
 • Allan Nyom (Kamaru)
 • Odion Ighalo (Nigeria)

AFC Bournemouth 3:

 • Christian Atsu (Ghana)
 • Tokelo Rantie (Afrika ta Kudu)
 • Max Gradel (Ivory Coast)