US Open: Andy Murray ya kai zagaye na 4

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana hasashen cewar Murray ne zai kai wasan zagayen gaba a kan Anderson

Andy Murray ya kai wasan zagaye na hudu a gasar kwallon tennis ta US Open, bayan da ya doke Thomaz Bellucci na Brazil.

Murray ya samu nasara ne a kan Bellucci wanda ke mataki na 30 a jerin 'yan wasan da suka fi iya kwallon tennis a duniya da ci 6-3 da 6-2 da kuma 7-5 a New York.

Dan wasan Birtaniya wanda ke matsayi na uku a jerin wadanda suke kan gaba a iya wasan tennis a duniya zai kara da Kevin Anderson na Afirka ta Kudu a ranar Litinin.

Murray ne ke kan gaba a yawan lashe wasa 5-1 a karawa da ya yi da Anderson, a watan Yuni ma da suka fafata a Queen Murray ne ya samu nasara.