Wikki ta casa Akwa United da ci 3-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Wasannin makwo na 28 a gasar Premier Nigeria da aka yi ranar Lahadi

Wikki Tourists ta samu nasara a kan Akwa United da ci 3-1 a gasar Premier Nigeria wasan makwo na 28 da suka fafata a ranar Lahadi.

Sauran sakamakwon wasannin da aka yi Nasarawa United da Warri Wolves tashi suka yi wasa kunnen doki, Giwa FC ta ci Enyimba kwallo daya mai ban Haushi.

Heartland kuwa doke Rangers ta yi 2-0, yayin da El-Kanemi Warriors ta zura wa Lobi Stars kwallaye 2-1, haka ma Shooting Stars ta ci Sunshine Stars kwallaye 2-1.

Taraba FC kuwa kwallaye 2-0 ta kwaso a wasan da ta bakunci IfeanyiUbah, sai Kwara United da ta doke Abia Warriors da ci daya mai ban haushi.

Sai a ranar Litinin ne za a yi gumurzu tsakanin Sharks da Kano Pillars a Fatakwal da kuma karawa tsakanin Dolphins da Bayelsa United.

Ga sakamakwon wasannin makwo na 28 da aka yi:

  • Giwa FC 1-0 Enyimba
  • FC IfeanyiUbah 2-0 FC Taraba
  • Nasarawa United 1-1 Warri Wolves
  • Kwara United 1-0 Abia Warriors
  • Shooting Stars 2-1 Sunshine Stars
  • El-Kanemi Warriors 2-1 Lobi Stars
  • Wikki Tourists 3-1 Akwa United
  • Heartland 2-0 Rangers