Damben Garba da Shagon Mada babu kisa

Image caption Garba Dan Malumfashi da Shagon Mada babu kisa a wannan takawar da suka yi

An ci gaba da wasan damben gargajiya da ake yi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria da sanyin safiyar Asabar.

An fara da damben da Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa, wanda ya kashe Shagon Ali Mai Maciji daga Kudu a turmi na biyu.

Sa zare da aka yi tsakanin Malam na 'Yar Ja daga Kudu da Bahagon Abba na Bacirawa daga Arewa babu kisa a turmi biyu da suka fafata.

Shi ma damben Shagon Yahaya daga Arewa da Matawallen Kwarkwada daga Kudu babu wanda ya yi nasara a turmi uku da suka yi gumurzu.

Shi kuwa Aminu Shagon Langa-Langa daga Arewa kashe Shagon Bahagon Sarka daga Kudu ya yi a turmi na biyu, kuma a dan karamin lokaci.

Damben Bahagon Bala Kada daga Arewa da Bahagon Sisco ya zo da gardama, tun farko Bahagon Bala ya kashe Sisco, amma Sisco ya ce bai fadi ba.

Suka sake karawa a turmi na biyu suka dunga kai wa juna duka sai ga Sisco a kasa wanwar, amma ya ce kwashe shi Bahagon Bala ya yi da kafa, hakan ya sa aka raba wasan.

Nan da nan aka shiga fili tsakanin Shagon Mada daga Kudu da Garba Dan Malumfashi daga Arewa kuma turmi uku suka yi babu kisa aka raba karawar.

An rufe fili ne da dambe tsakanin Autan Faya daga Kudu da Bahagon Audu Argungu daga Arewa kuma turmi biyu suka yi aka raba wasan aka kuma tashi daga wasa.