Euro 2016: Scotland za ta kara da Jamus

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Faransa ce za ta karbi bakuncin wasannin da za a yi a 2016

Scotland za ta karbi bakuncin Jamus a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a ranar Litinin.

Karawar da za su yi Hampden Park a wasan rukuni na hudu, Jamus ce ke kan gaba a rukunin da maki 14, a inda Scotland tana mataki na hudu da maki 11.

A karawar farko da suka fafata Jamus ce ta samu nasara da ci 2-1 a gida.

Ga sauran wasannin da za a yi ranar Litinin:

  • Armenia vs Denmark
  • Scotland vs Germany
  • Ireland vs Georgia
  • Albania vs Portugal
  • Northern Ireland vs Hungary
  • Poland vs Gibraltar
  • Romania vs Greece
  • Finland vs Faroe Islands