Yarima Ali zai sake takarar kujerar Fifa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karo na biyu da Yarima Ali zai sake takarar kujerar Fifa

Yarima Ali Bin Hussein na Jordan na shirin bayyana aniyarsa ta sake yin takarar kujerar shugabancin hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa a ranar Laraba.

A fafatawar da ya yi da Sepp Blatter a zaben hukumar da aka yi a watan Mayu, Ali ya samu kuri'u 73 da hakan ya sa aka yi zabe zagaye na biyu, kafin daga baya ya janye daga takarar.

Ali zai fafata da shugaban hukumar kwallon kafar nahiyar Turai Michel Platini da kuma tsohon babban jami'in hukumar Chung Mong-joon.

Nahiyar Afirka tana da kuri'u 54 daga cikin 209 da mambobin kasashe FIFA za su kada a zaben shugaban da za a yi ranar 26 ga watan Febrairun.

Hukumar za ta sake zaben wanda zai shugabanci hukumar ne, saboda zargin cin hanci da rashawa da ya mamaye Fifa, duk da zaben Sepp Blatter karo na biyar da aka yi a watan Mayu.