Sharks ta doke Kano Pillars da ci 1-0

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Sharks da ci 1-0 a wasan mako na 28

Sharks ta samu nasara a kan Kano Pillars da ci daya mai ban haushi a gasar Premier Nigeria wasan mako na 28 da suka kara a Fatakwal ranar Litinin.

Sharks ta zura kwallo ne ta hannun Daniel Jackson a minti na 17 da dawo wa daga hutun rabin lokaci.

Haka shi kuwa wasan da aka buga tsakanin Dolphins da Bayelsa United a ranar Talata, Dolphins ce ta lashe wasan da ci 2-0.

Dolphins din ta fara cin kwallo a minti 10 da fara wasa ta hannun Ebitimi Agogu, sannan ta kara ta biyu a minti na 25 da dawo da gada hutu ta hannun Wilson Andoh.

Rashin nasarar da Kano Pillars ta yi ya sa tana mataki na tara a kan teburi da maki 40, yayin da Sharks ta hada maki 32 ta kuma koma ta 16 a teburin.

Kano Pillars za ta karbi bakuncin Abia Warriors a wasan mako na 29 a jihar Kano, Nigeria, a inda Ifeanyi Uba za ta ziyarci Sharks a Fatakwal.

Har yanzu Enyimba ce a mataki na daya a kan teburi da maki 52, sai Warri Wolves da maki 48 a matsayi na biyu, yayin da Sunshine Stars ta hada maki 47 a mataki na uku a kan teburin.