An zura kwallaye 598 a raga a Premier Nigeria

Hakkin mallakar hoto lmgnfpl twitter
Image caption Ranar Lahadi za a ci gaba da wasannin mako na 29 a gasar Premier Nigeria

An ci kwallaye 598 a gasar Premier Nigeria bayan da aka kammala wasannin mako na 28 a ranar Litinin.

Enyimba ce ke mataki na daya a kan teburin gasar da maki 52, sai Warri Wolves ta biyu da maki 48, Sunshine Stars tana da maki 46 a matsayi na uku sai Wikki ta hudu da maki 46.

Kano Pillars kuwa wacce ke rike da kofin bara tana matsayi na tara da maki 40.

Dolphins tana sahun 'yan hudun karshen teburi da maki 31 a mataki na 17, sai Akwa United ita ma mai maki 31 a matsayi na 18, yayin da Taraba ce ta 19 da maki 26, sai Bayelsa United ta karshe da maki 23.

Za kuma a ci gaba da buga wasannin mako na 29 a ranar Lahadai 13 ga watan Satumba.