'Yan kwallon kafa ne ke wawure kudade

Image caption Sai a watan Janairun 2016 ne za a sake buge kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula

Wani bincike da Fifa ta yi ta ce Albashin da ake biyan 'yan kwallon kafa ne ke daukar kaso mafi tsoka a lokacin da aka sayi 'yan wasan tamaula a shekaru biyu da suka wuce.

A binciken da ta gudanar tun daga shekarar 2013, ta gano cewar 'yan wasan tamaula da aka sayo daga wasu kungiyoyi sun karbi kaso 57 cikin dari na cinikayyar da aka yi.

Kashi 41 ne gundarin kudin saye da sayar da 'yan kwallon da aka yi, yayin da kudin masu kula da harkar tamaular 'yan wasa ya ci gaba da zama kaso biyu daga cikin 100.

Kuma kaso hudu daga cikin kudaden da kungiyoyin Turai suka kashe sun biya albashin 'yan wasa ne a lokacin da aka yi cinikayyar 'yan kwallon.

Binciken da aka yi daga tsakanin shekaru biyu ya nuna an biya 'yan kwallo albashin $16.5bn, a inda $12bn aka kashe kan saye da sayar da 'yan wasa, kuma $700m aka bai wakilan 'yan kwallon.