An zargi FA da kin cewa komai kan Carneiro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya dage da cewar Eva Carneiro and Jon Fearn sun aikata ba dai-dai ba

An zargi hukumar kwallon kafar Ingila da kin cewa komai kan matakin da Chelsea ta dauka a kan likita Eva Carneiro.

Har yanzu Dr Carneiro ba ta dawo kan aikinta ba, bayan da koci Jose Mourinho ya zarge ta da rashin iya aiki.

Mourinho ya soki Dr Eva Carneiro da Jon Fearn bisa kai dauki da suka yi wa Eden Hazard a wasan da suka buga 2-2 da Swansea, hakan sai da ya sa dan wasan ya bar cikin fili domin a duba lafiyarsa.

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ce wannan matsalar cikin gida ce, saboda haka su kadai ne za su warware ta.

Mourinho ya kuma tsaya kai da fata kan cewa an aikata ba dai-dai ba a yadda Carneiro da Fearn suka kai wa Hazard dauki a fili har aka fitar da dan wasan wajen fili a karawa da Swansea ranar 8 ga watan Agusta.

Hakan ne ya kuma sa Chelsea ta karasa fafatawar da 'yan wasa tara a cikin fili, wanda tun farko an bai wa Thibaut Courtois jan kati a wasan.