Ba zan gayyaci Adebayor tawagar Togo ba - Saintfiet

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Adebayor bai buga wa Tottenham kwallo tun fara kakar wasannin bana

Kocin tawagar kwallon kafar Togo, Tom Saintfiet ya ce ba zai sake gayyatar Emmanuel Adebayor domin ya buga wa kasar tamaula ba.

Saintfiet ya ce ya yanke wannan hukuncin ne saboda kin amsa kiran waya da dan wasan ya yi domin buga karawar da suka yi da Djibouti ranar 4 ga watan Satumba a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

A watan Yuni Adebayor ya yi ikirarin kaurace wa kasar daga buga mata kwallo, bayan da aka cire shi daga matsayin kyaftin din tawagar kasar.

Adebayor bai bayar da amsa ga mahukuntan kwallon kafar Togo kan gayyatar da kocin ya yi masa ko da ta hanyar tura sakon waya ko ta internet ba in ji Saintfiet.

Kocin ya kara da cewar yana ganin Adebayor ba shi da sha'awar cigaba da buga wa Togo Tamaula.

Adebayor bai buga wa Tottenham wasa ba tun fara kakar gasar bana, kuma ba ya cikin 'yan wasan da za su buga wa kungiyar wasannin Premier da na Europa.