De Gea na fatan dawo da tagomashinsa

Image caption David De Gea bai buga wa Manchester United wasa a kakar bana ba

Mai tsaron ragar Manchester United ya ce yana jin dadin zama a kungiyar kuma yana fatan zai dawo da tagomashinsa a kokarin da yake yi na dawowa buga mata kwallo.

De Gea mai shekaru 24, bai buga wa United tamaula a bana ba, yayin da Louis van Gaal ya ce golan yana bukatar natsuwa saboda zawarcinsa da Real Madrid ta yi masa a lokacin.

Sai dai kuma De Gea ya fara buga babban wasa a bana, a inda ya buga wa tawagar kwallon kafar Spaniya wasa da ta yi da Macedoniya a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a ranar Talata.

Kiris ya rage De Gea ya koma Madrid da taka leda a bana, bayan da United ta amince da golan ya koma Spaniya da wasa, amma kungiyoyin biyu suka makara wajen saka hannu kan yarjejeniya.

Sabon mai tsaron raga da United ta dauko dan kasar Argentina Sergio Romero ne yake buga wa kungiyar wasanni.