All African Games: Nigeria ta doke Ghana 2-0

Image caption Nigeria ta samu maki uku a wasan da ta yi da Ghana kenan

Matasan tawagar kwallon kafar Nigeria 'yan kasa da shekaru 23 sun doke na Ghana da ci 2-0 a gasar wasannin Afirka da ake yi a Congo Brazzaville.

Nigeria ta zura kwallon farko ne a raga ta hannun Junior Ajayi a minti na 10 da dawo wa daga hutun rabin lokaci, sannan Kingsley Sokari ya kara ta biyu saura minti uku a tashi daga wasan.

A wasan farko Nigeria ba ta kara da Masar ba, saboda janyewa da tayi daga gasar daf da za a fara wasannin, ita kuwa Ghana ta tashi wasa canjaras ne da Senegal wato 0-0 a ranar Lahadi.

Nigeria za ta buga wasan gaba da Senegal a ranar Asabar, yayin da Ghana ta kammala wasannin rukuni na biyu da maki daya kacal.

Daf da karshen watan Agusta Masar din ta ce ta janye tawagar kwallon kafa ta mata da kuma ta maza daga shiga wasannin na Afirka ba tare da ta bayar da wani dalili ba.