Rooney ya kafa tarihi a kwallon kafa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rooney ya ce ya dade yana son kafa wannan tarihi.

Dan wasan Ingila, Wayne Rooney, ya kafa tarihin zaman dan wasan kasar da ya fi zura kwallo a raga, inda ya ci kwallaye 50.

Rooney ya ci kwallo ta 50 ne a bugun fenareti a wasan da Ingila ta doke Switzerland da ci 2-0 domin nema cancantar shiga gasar Zakarun Turai ta shekarar 2016.

Dan wasan na Manchester United mai shekaru 29 a duniya, ya ce wannan tarihi ne da ya dade yana begen sa.

A baya dai, dan wasan Ingila, Sir Bobby Charlton ne ya kafa tarihin zama dan kasar da ya fi zura kwallaye -- kuma shekaru 45 ya yi babu wanda ya kamo shi.