Courtois na bukatar tiyata - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Thibaut Courtois ne babban golan Chelsea

Golan Chelsea Thibaut Courtois, na bukatar tiyata a gwiwarsa kuma zai yi jinya mai tsawo, in ji kocinsa Jose Mourinho.

Dan kwallon mai shekaru 23, ya ji raunin ne a lokacin horo a ranar Laraba.

"Mun gamu da cikas, saboda babu dadi ka rasa babban golanka," in ji Mourinho.

Tsohon golan Stoke, Asmir Begovic ne zai maye gurbin Courtois.

Bayan shafe kakar wasa har uku a matsayin aro tare da Atletico Madrid, Courtios ya dawo Chelsea a kakar wasa ta bara inda ya shiga gaban Petr Cech.