Manchester United ta doke Liverpool 3-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne wasan farko da Martial ya fara buga wa United

Manchester United ta samu nasara a kan Liverpool da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na biyar da suka kara a Old Trafford ranar Asabar.

Danny Blind ne ya fara cin kwallo a minti hudu da dawowa daga hutun rabin lokaci, sannan Ander Herrara ya kara ta biyu a bugun fenariti.

Saura minti shida a tashi daga wasan Liverpool ta zare kwallo daya ta hannun Christian Benteke.

Sai dai kuma United ta kara kwallo ta uku ta hannun sabon dan wasa da ta sayo Anthony Martial mai shekara 19 daga Monaco saura minti hudu a tashi daga karawar.

Da wannan sakamakon United tana mataki na biyu a teburin Premier da maki 10, yayin da Liverpool take matsayi na tara da maki bakwai a kan teburin.