Kano Pillars ta ci Abia Warriors 3-0

Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Kano Pillars tana da maki 43 bayan wasanni 29 da ta yi a gasar Premier

Kano Pillars ta doke Abia Warriors da ci 3-0 a gasar Premier Nigeria wasan mako na 29 da suka kara a ranar Lahadi.

Pillars ta zura kwallayen ne ta hannun Ubong Ekpai da Azeez Shobowae da kuma Nafiu Ibrahim da hakan ya bai wa kungiyar damar hada maki uku a karawar.

Sauran wasannin da aka buga Enyimba ta doke Dolphins da ci 2-0, yayin da Lobi Stars da Wikki Tourist suka tashi wasa kunnen doki 1-1, Sharks doke Ifeanyiubah ta yi da ci 1-0.

Nasarawa United kuwa kwallaye 3-2 ta ci Sunshine Stars har gida, sai Warri Wolves da ta zurawa Kwara United 3-0

Tun a ranar Asabar Bayelsa United ta ci El-Kanemi Warriors 4-1 a karawar da suka yi a Oghara.

Ga sakamakon wasannin mako na 29 da aka buga:

  • Sharks 1-0 FC Ifeanyiubah
  • FC Taraba 1-0 Giwa FC
  • Enyimba 2-0 Dolphins
  • Lobi Stars 1-1 Wikki
  • Akwa Utd 1-0 Heartland
  • Rangers 2-1 Shooting Stars
  • Sunshine Stars 2-3 Nasarawa Utd
  • Wolves 3-0 Kwara Utd
  • Bayelsa Utd 4-1 El-Kanemi