Caf U23: An raba jadawalin gasar matasa

Image caption Kasashe uku ne za su wakilci Afirka a gasar Olympic da za a yi a Brazil a 2016

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta raba jadawalin wasannin kwallon kafa na matasa 'yan kasa da shekara 23 a ranar Litinin a Alkahira, babban birnin Masar.

Hukumar ta raba jadawalin ne domin fitar da kasashe uku da za su wakilci nahiyar a wasan kafa a gasar Olympic da Brazil za ta karbi bakunci a 2016.

Rukunin farko ya kunshi Senegal da Afirka ta Kudu da Zambia da kuma Tunisia.

Rukuni na biyu kuwa ya hada ne da Masar da Algeria da Mali da kuma Nigeria.

Filaye biyu ne za su karbi bakuncin wasannin a Senegal da suka hada dana Dakar da kuma na M'Bour.

Za kuma a fara gasar ne daga 28 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Disambar 2015.