Rooney ba zai buga karawa da PSV ba

Image caption Van Gaal ya ce ya kamata Rooney ya yi jinya domin tunkarar wasan gaba

Wayne Rooney ba zai buga wa Manchester United wasan gasar cin kofin zakarun Turai da za ta kara da PSV Eindhoven ranar Talata ba, saboda raunin da ya ji.

Rooney mai shekaru 26, bai buga gasar Premier da Manchester United ta doke Liverpool da ci 3-1, sakamakon raunin da ya ji a filin atisaye.

Kocin United Louis van Gaal ya ce ba zai yi gangancin saka Rooney a wasan da za su kara da PSV ba, domin yana bukatar ya murmure kafin wasan da United za ta yi na gaba.

Sai dai 'yan wasan da suka hada da James Wilson da kuma Andreas Pereira suna daga cikin wadanda United ta tafi da su Netherlands.

Karawar da United za ta yi da PSV a ranar Talata shi ne wasan farko da za ta fafata na cikin rukuni na biyu a gasar bana.