Djokovic ya lashe Gasar US Open

Image caption Djokovic bai yi ko gezau ba duk da goyon bayan da 'yan kwallo ke nuna wa Federer.

Zakaran Tennis na duniya, Novak Djokovic ya lashe gasar kwallon tennis ta US Open a karo na biyu, bayan da ya doke abokin karawarsa, Roger Federer ranar Lahadi.

Dan kasar ta Serbia ya doke abokin karawar sa ne da ci 6-4 5-7 6-4 6-4 a birnin New York, kuma zai kammala wannan shekarar da manyan Kofunan Tennis guda uku cikin hudu da ake ji da su.

Djokovic, mai shekaru 28, bai yi ko gezau ba duk da cewa akasarin 'yan kallo sun rika nuna goyon bayansu ga Federer.

Federer, mai shekaru 34, ya yi fatan doke Djokovic domin samun Kofi na 18 a cikin manyan Kofunan Gasar, amma hakan bai yiwu ba.