Mertesacker ba zai buga karawa da Dinamo ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Laraba Arsenal za ta kara da Dinamo Zagreb

Dan kwallon Arsenal mai tsaron baya Per Mertesacker ba zai buga wasan da za su yi da Dinamo Zagreb sakamakon raunin da ya ji.

Arsenal za ta ziyarci Dinamo Zagreb a wasan gasar cin kofin zakarun Turai da za su kara a ranar Laraba.

Mertesacker ya ji rauni ne a wani hadarin mota da ya rutsa da shi a ranar Litinin.

Haka su ma Jack Wilshere da kuma Danny Welbeck ba za su buga wa Arsenal wasan ba.

Sai dai kuma ana sa ran Theo Walcott zai buga wa Arsenal karawa da Dinamo wacce rabonta da shiga gasar shekaru biyu da suka wuce kenan