Juventus ta doke Man City 2-1 a Ettihad

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasan farko na cikin rukuni da aka doke Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai kenan

Manchester City ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Juventus a gasar cin kofin zakarun Turai da suka buga a Ettihad ranar Tatata.

Manchester City ce ta fara zura kwallo ta hannun kyaftin dinta Vincent Kompany a minti na 12 da dawo wa daga hutun rabin lokaci.

Juventus ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Mario Mandzukic, sannan Alvaro Morata ya kara ta biyu a ragar City saura minti tara a tashi daga karawar.

Ga sakamakon wasannin da aka buga a ranar Talata:

  • Real Madrid 4 - 0 Shakt Donsk FT
  • PSV 2 - 1 Man Utd
  • Paris St G 2 - 0 Malmö FF
  • VfL Wolfsburg 1 - 0 CSKA
  • Benfica 2 - 0 FC Astana
  • Galatasaray 0 - 2 Atl Madrid
  • Sevilla 3 - 0 Borussia Mönchengladb