Shaw ya karye a wuri biyu a kafarsa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shaw ya sha kuka

Dan kwallon Manchester United, Luke Shaw ya samu karaya a wuri biyu a kafarsa a wasan da United ta sha kaye a hannun PSV Eindhoven a gasar zakarun Turai.

Ana saran Shaw mai shekaru 20 zai yi jinya mai tsawo sakamakon karayar.

Ya ji rauni ne bayan da Hector Moreno ya kai masa hara, kuma sai da ya shafe mintuna 10 ana ba shi agajin gaggawa kafin ya bar cikin filin.

"Abin babu dadi. Yadda aka kai masa hari bai dace ba. Ya sha kuka sosai saboda raunin," in ji kocinsa Louis van Gaal.