U23: Burkina Faso ta doke Nigeria 3-1

Image caption Tawagar Nigeria ta maza da ta mata za ta buga wasan neman tagulla a gasar wasannin Afirka

Tawagar kwallon kafar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Burkina Faso ta doke ta Nigeria da ci 3-1 a gasar wasannin Afirka da Congo Brazaville ke karbar bakunci.

Da wannan sakamakon Burkina Faso ta kai wasan karshe kenan, kuma za ta kara da Senegal.

Senegal ta kai wasan karshe ne a gasar bayan da ita ma ta doke Congo da ci 3-1.

Haka kuma a wasannin mata Kamaru ta kai wasan karshe bayan da ta doke Nigeria da ci 2-1.

Kamarun za ta fafata a wasan karshe da Ghana ne wacce ta samu nasara a kan Ivory Coast da ci daya mai ban haushi.