Browne Jr ya mutu bayan damben boksin

Hakkin mallakar hoto facebook
Image caption Browne ya mutu ne sakamakon dukan da ya sha a hannun Magali

Wani dan damben boksin dan kasar Austalia ya mutu kwanaki hudu bayan da a ka doke shi ya fadi magashiyan a karawar da ya yi a Sydney.

Carlo Magali na Philippines ne ya yi wa Davey Browne Jr mai shekaru 28, bugun kwaf daya a turmi na 12.

Browne mahaifin yara biyu ya kasa farfado wa daga suman da ya yi, dalilin da ya sa na'urar da take taimaka masa yin numfashi ta kashe kanta.

Kungiyar likitocin Australia ta yi kira da a soke wasan damben boksin sakamakon mutuwar da Browne din ya yi.

Browne ya mutu ne watanni shida bayan da wani dan damben Australia Braydon Smith na Queensland ya fadi a filin dambe ya mutu a gasar cin kambun matsakaita nauyi wato featherweight a garinsa na Toowoomba.