2024 Olympics: Birane biyar ke takara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cikin watan Satumbar 2017 ne za a zabi birnin da zai karbi bakuncin gasar 2024

Birane biyar ne suke tararar karbar bakuncin wasannin Olympics da za a yi a lokacin bazara a shekarar 2024.

Biranen sun hada da Los Angeles da Hamburg da Rome da Budapest da kuma Paris.

A cikin watan Satumbar 2017 'yan ne kwamitin gasar za su zabi birnin da zai karbi bakuncin wasannin a Lima ta Peru.

Haka kuma kwamitin wasannin ya sauya doka a watan Agusta domin tabbatar da cewar duk biranen da suka yi takara za su kai ranar da za a zabi wanda ya yi nasara.

A baya kwamitin ya kan zabo wasu daga cikin wadanda suka fi yin fice wajen kokarin takarar karbar bakuncin wasannin, sannan mambobin kasashen gasar su 100 su fitar da wanda za a bai wa damar.