Raunin da na ji ba mai girma ba ne - Kompany

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Juventus da ci 2-1 a Ettihad

Kyaftin din Manchester City, Vincent Kompany ya ce raunin da ya ji a karawar da suka yi da Juventus ba mai girma ba ne.

Juventus ce ta doke Manchester City da ci 2-1 a wasan gasar cin kofin zakarun Turai da suka yi a ranar Talata a Ettihad.

An sauya Kompany mai shekaru 29, a minti na 75 daga fili sakamakon raunin da ya ji.

Kompany ya ce ya fita daga wasan ne domin ka da raunin ya iya muni kafin a tashi daga wasan.

Manchester City wacce take mataki na daya a kan teburin Premier za ta kara da West Ham a ranar Asabar, kuma Manuel Pellegrini ya ce Kompany zai buga masa wasan.