An raba jan kati 49 a gasar Premier Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sauran wasanni tara a kammala gasar Premier bana

Alkalan wasan gasar Premier na Nigeria sun bai wa kimanin 'yan wasa 49 jan kati, sannan suka bayar da katin gargadi sau 1,017.

A ranar Lahadi aka kammala buga wasannin mako na 29 a gasar, yayin da aka zura kwallaye 624 a wasannin.

Kungiyar Akwa United ce kan gaba a matsayin wacce ta fi karbar jan kati a gasar a inda ta karbi guda bakwai.

Giwa FC ita ce ta biyu da aka bai wa 'yan wasanta jan kati sau biyar, kungiyoyin Dolphins da Warri Wolves da Bayelsa United sune suke mataki na uku a inda aka korar musu 'yan wasa sau hudu kowannensu.

Kulob din Dolphins shi ne kan gaba wajen karbar katin gargadi a inda ya karbi 65, sai Enyimba da ta karbi 63 a matsayi na biyu.

Warri Wolves ce a mataki na uku a yawan karbar katin gargadi a inda ta karbi 62, yayin da Giwa FC da Taraba United kowannensu ya karbi 59.