''Na manta yadda ake ji in an ci wasa''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea dai sun shiga filin wasan ne cikin matsin lamba.

Manajan kulob din Chelsea Jose Mourinho ya ce har ya manta da farin cikin da ake ji idan an ci wasa bayan nasarar ci 4-0 da ya samu kan Maccabi Tel aviv daren Laraba.

Mourinho dai na mayar da martani ne kan farfadowar da kulob dinsa ya yi daga rashin nasarar da ya yi ta cin karo da ita a farkon gasar Premier ta bana.

''Na manta yadda ake ji, domin an dauki lokaci mai tsawo ba mu ci wasa ba, yadda ake jin akwai faranta rai'' in ji Mourinho.

Duk da barar da bugun fenariti da Eden Hazard ya yi a farkon wasan, kwallayen da Willian da Oscar da Diego Costa da kuma Fabregas suka ci; sun tabbatar da cewa kulob din bai samu wata matsala ba wajen doke abokin karawarsa daga Isra'ila.

Karin bayani