Amokachi ya raba-gari da FC Ifeanyi Ubah

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amokachi bai ji dadin barin kungiyar ba

Tsohon kyaftin din Nigeria, Daniel Amokachi ya raba-gari da kungiyar FC Ifeanyi Ubah a matsayin kocin tawagar bayan shafe makonni biyar a kungiyar.

Dan shekaru 42 ya nuna sha'awarsa a baya, domin samun nasarori a kungiyar.

Sai dai rashin samun sakamako mai kyau ya janyo rashin jituwa tsakaninsa da mai kungiyar.

"Abin takaici ne zan bar wannan kungiyar bayan gajeren lokaci," in ji Amokachi.

Ya kara da cewar "Na dade ina sha'awar wannan kulob din da kuma manufar kungiyar wajen samun ci gaba."

Rahotanni sun nuna cewa Amokachi ya nuna rashin gamsuwarsa ne game da tsarin kungiyar na yin tafiya a cikin dare a mota idan suka buga wasa a wani sashen kasar.

Abin da kuma shi mai kungiyar watau Attajiri, Mr Ifeanyi Ubah ya kallo a matsayin rashin biyayya.