Ba zan fita daga Switzerland ba - Blatter

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blatter na shan matsin lamba

BBC ta samu labarin cewa shugaban hukumar kwallo kafa ta duniya, FIFA Sepp Blatter, ya fada wa abokan aikinsa cewa ba zai fita daga cikin Switzerland.

Ya bayyana haka ne a yayin da ake ci gaba da wani bincike a kan hukumar kwallon kafar bisa zargin cin hanci da rashawa.

A ranar Juma'a ne ya kamata Mr Blatter ya je wajan biki a Moscow na cika kwanaki dubu daya kafin soma gasar kwallon kafa ta duniya da Rasha za ta dauki bakunci a shekarar 2018.

Wakilin BBC ya ce a watan Yuli Mr Blatter ya ce ba zai yi abin da ya kira ganganci na yi tafiya ba, bayan ana ci gaba da bincike a kan wasu zarge-zarge da Amurka ke yi wa wasu shugabannin hukumar ta FIFA.

Hakan na zuwa ne bayan da Fifa ta dakatar da sakatarenta Jerome Valcke daga aiki har sai-baba-ta-gani bisa zarginsa da hannu wajen sayar da tikitin wasannin kwallon kafa ta duniya da aka yi a bara a kan farashin da ya wuce wanda aka amince da shi.