Fifa ta dakatar da Jerome Valcke

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin Vackle da sayar da tikitin wasa ba bisa ka'ida ba.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniyaFIFA, ta dakatar da sakatare janar din ta, Jerome Valcke daga aiki har sai-baba-ta-gani.

Kwamitin tabbatar da da'a na hukumar zai yi bincike a kan wasu rahotanni da aka fitar a ranar Alhamis, inda ake zargin Mr Valcke da hannu wajen sayar da tikitin wasannin kwallon kafa ta duniya da aka yi a bara a kan farashin da ya wuce wanda aka amince da shi.

Sai dai Mr Valcke ya musanta wannan zargi.

BBC ta fahimci cewa an hana jirgin Mr Valcke wanda ke hanyarsa Moscow, inda ya koma Zurich bayan an sanar da dakatar da shi.