Chelsea ta doke Arsenal da ci 2-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea ta hada maki bakwai daga wasanni shida da ta buga

Chelsea ta samu nasara a kan Arsenal da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na shida da suka kara a Stamford Bridge ranar Asabar.

Chelsea ta ci kwallayenta biyu ta hannun Kurt Zouma da kuma Eden Hazard da hakan ya ba ta damar samun maki uku a karawar.

Arsenal ta kammala fafatawar da 'yan wasa tara a cikin fili, bayan da aka kori Gabriel da kuma Santi Cazorla daga wasan.

Chelsea za ta ziyarci Manchester United a wasan mako na 7, yayin da Leicester za ta karbi bakuncin Arsenal.