Jordan Henderson ya karye a kafa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Henderson zai yi jinyar makonni bakwai kafin ya dawo murza leda

Dan kwallon Liverpool, Jordan Henderson, zai yi jinya makwonni bakwai bayan da ya karye a kafarsa ta hagu.

Henderson mai shekaru 25, ya ji rauni ne a lokacin da yake yin atisaye, za kuma a yi masa aiki a kafar ranar Litinin.

Dan wasan ba zai buga wa Liverpool wasanni 11 da za ta buga a karawa daban-daban ba.

Haka kuma Henderson ba zai buga wa Ingila karawar da za ta yi da Estonia a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ranar 9 ga watan Oktoba da kuma na Lithuania a ranar 12 ga watan Oktoba ba.

Da kyar ne idan Henderson zai iya buga wasan sada zumunta da Ingila za ta yi da Spaniya da kuma Faransa a watan Nuwamba.