West Ham ta doke Man City a Ettihad

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption West Ham ta koma mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 12

Manchester City ta kwashi kwallaye 2-1 a hannun West Ham a gasar Premier wasan mako na 6 da suka kara a Ettihad a ranar Asabar.

Victor Moses dan wasan Chelsea dake bugawa West Ham wasa aro ne ya ci kwallon farko a minti na shida da fara tamaula.

A minti na 31 ne kuma Diafra Sakho ya ci wa West Ham kwallo ta biyu tun daga tazarar yadi shida.

Daf da za'a tafi hutu ne sabon dan kwallon da Manchester City ta sayo Kevin De Bruyne ya zare kwallo daya da aka zura mata.

Manchester City tana nan a matakinta na daya a kan teburi da maki 15, Yayin da West Ham ta koma ta biyu a teburin da maki 12.

West Ham za ta karbi bakuncin Norwich a wasan mako na 7, yayin da Manchester City za ta ziyarci Tottenham a White Hart Lane.