Real Madrid ta ci Granada 1-0 a La Liga

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Real Madrid ta hada maki 10 daga wasanni hudu da ta yi a gasar La Liga

Real Madrid ta samu nasara a kan Granada da ci daya mai ban haushi a gasar La Liga wasan mako na hudu da suka yi a ranar Asabar.

Madrid ta ci kwallon ne a minti na biyar da dawo wa daga hutun rabin lokaci ta hannun Karim Benzema.

Da wannan sakamakon Madrid ta hada maki 10 daga wasanni hudun da ta buga, kuma tana mataki na daya a kan teburi kafin Barcelona ta yi wasa.

Barcelona wacce ke da maki tara a wasanni uku da ta buga, za ta karbi bakuncin Levante a Nou Camp ranar Lahadi.

Real Madrid za ta ziyarci Athletico Bilbao a gasar mako na biyar a ranar 23 ga watan Satumba.