El-Kanemi ta doke Enyimba da ci 2-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sauran wasannin takwas kenan a kammala gasar bana

El-Kanemi Warriors ta ci Enyimba International 2-1 a gasar Premier Nigeria wasannin mako na 30 da suka yi a ranar Lahadi.

Sauran sakamakon fafatawar da aka yi Wikki Tourist ta doke Bayelsa United da ci 2-0, Nasarawa United kuwa ci daya mai ban haushi ta doke Enugu Rangers.

Kano Pillars kuwa kunnen doki ta buga a gidan Ifeanyiubah, sai karawar da Kwara United ta yi rashin nasara a gida a hannun Sunshine Stars da ci 2-1.

Ga sakamakon wasannin mako na 30 da aka buga:

  • Giwa FC 1-0 Sharks
  • Dolphins 3-1 FC Taraba
  • El-Kanemi 2-1 Enyimba
  • Wikki 2-0 Bayelsa United
  • Heartland 0-0 Lobi Stars
  • Nasarawa Utd 1-0 Rangers
  • Abia Warriors 2-1 Wolves
  • FC Ifeanyiubah 1-1 Kano Pillars
  • Shooting Stars 1-0 Akwa Utd
  • Kwara Utd 1-2 Sunshine Stars