FA ta tuhumi Costa da ta da yamutsi a wasa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Hukumar ta bai wa Costa nan da ranar Talata domin ya kare kansa

FA ta tuhumi Diego Costa na Chelsea da tayar da yamutsi a wasan mako na shida na gasar Premier da kungiyar ta buga ranar Asabar.

Chelsea ce ta samu nasara da ci 2-0 a karawar da ta karbi bakuncin Arsenal a Stamford Bridge.

Costa ya mari mai tsaron bayan Arsenal Laurent Koscielny sannan ya yi cacar baki da Gabriel har sai da alkalin wasa Mike Dean ya kore shi daga wasan.

Haka kuma hukumar ta tuhumi Gabriel da nuna halayyar rashin da'a, sannan ta tuhumi kungiyoyin biyu da kasa tsawatarwa 'yan wasan nasu.

An bai wa Costa daga nan zuwa ranar Talata 22 ga watan Satumba domin ya kare kansa daga zargin da hukumar ke yi masa.

Shi kuwa Gabriel an ba shi nan da ranar Alhamis 24 ga watan Satumba da kuma kungiyoyin biyu su amsa tuhumar da aka yi musu.