An ci kwallaye 644 a gasar Premier Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a ci gaba da wasannin mako na 31 a ranar 27 ga watan Satumba

Kwallaye 644 aka zazzaga a raga a gasar Premier ta Nigeria, bayan da aka buga wasannin mako na 30 a ranar Lahadi.

Jumullar kungiyoyi 20 na gasar sun fafata a tsakaninsu sau 300, Kuma dan wasan Nasarawa United Esosa Igbinoba, shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye, a inda ya zura 14 a raga.

Tunde Adeniji na Sunshine Stars shi ne a mataki na biyu a wanda ya ci kwallaye 13, sai Bright Ejike na Heartland wanda ya zura kwallaye 12 a raga.

'Yan wasa uku ne suka zura kwallaye goma-goma a gasar da suka hada da Gbolahan Salami na Warri Wolves da Chisom Chikatara na Abia Warriors da Anthony Okpotu na Lobi Stars da kuma dan wasan Wikki Tourist Mubarak Umar.

Sauran wasanni takwas a kammala gasar bana, kuma za a ci gaba da wasannin mako na 31 a ranar Lahadi 27 ga watan Satumba.