An soke jan katin da aka bai wa Gabriel

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption FA tana tuhumar Gabriel da nuna halin rashin da'a a karawar

Hukumar kwallon kafar Ingila ta soke jan katin da aka bai wa Gabriel a karawar da suka yi da Chelsea, bayan da Arsenal ta shigar da korafi.

Hakan na nufin Gabriel wanda tun farko aka yanke masa hukuncin dakatar da shi daga buga wasanni uku zai ci gaba da buga wa Arsenal tamaula.

Sai dai kuma hukumar ta tuhumi dan kwallon da nuna halin rashin da'a, kuma tana sa ran zai kare kansa nan da ranar Alhamis.

Lokacin da aka bai wa Gabriel jan kati a wasan bai bar filin nan take ba, hakan ne ma yasa zai fuskanci hukunci daga hukumar.

Chelsea ce ta doke Arsenal da ci 2-0 a gasar Premier da suka buga a Stamford Bridge a gasar Premier ranar Asabar.