Fifa: An soma bincike kan Blatter

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Blatter ya ce zai sauka daga kujerarsa a watan Fabarairu

Masu shigar da kara na gwamnatin Switzerland sun soma gudanar da bincike a kan shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya-FIFA, Sepp Blatter.

Ofishin babban lauyan gwamnatin kasar, ya ce an tuhumarsa bisa zargin yin zamba a shugabancinsa da kuma salwantar da dukiyar da ba ta shi ba.

Bayanai sun ce Blatter na can na amsa tambayoyi daga lauyoyi.

Tuni Fifa ta dage taron manema labarai da ta shirya yi a shalkwatarta da ke Zurich.

Sakatare Janar na Fifa, Jerome Valcke a cikin wannan watan ya yi murabus bisa zargin wata badakala a hukumar.

Jami'an Fifa da dama na fuskantar tuhumar game da zargin cin hanci da rashawa a Amurka.