Newcastle da Chelsea sun tashi wasa 2-2

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea tana mataki na 15 a kan teburin Premier

Newcastle United ta buga 2-2 da Chelsea a gasar cin kofin Premier wasan mako na bakwai da suka yi a St James Park ranar Asabar.

Newcastle ce ta fara zura kwallaye biyu ta hannun Perez saura minti uku aje hutu da kuma ta biyu ta hannun Wijnaldum minti 15 da dawowa daga hutun.

Chelsea ta farke kwallayen da aka ci ta ta hannun Ramires da kuma Willian wanda ya ci saura minti hudu a tashi daga wasan.

Da wannan sakamakon Chelsea tana Matsayi na 15 a kan teburin Premier da maki takwas.

Newcastle United kuwa tana mataki na 19 da maki uku a kan teburin na Premier.