Tottenham ta ci Manchester City 4-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham ta hada maki 12 a gasar Premier daga wasanni 7 da ta yi

Tottenham ta doke Manchester City da ci 4-1 a gasar Premier wasan mako na bakwai a ranar Asabar.

City ce ta fara zura kwallo ta hannun sabon dan kwallon da ta sayo a bana Kevin de Bruyne, sai Eric Dier ya farkewa Tottenham kwallon daga bugun yadi na 25.

Daga nan ne Toby Alderweireld ya ci wa Tottenham kwallo ta biyu, sai Kane ya kara ta uku kuma kwallon farko da ya ci wa kulob din a kakar bana.

Erik Lamela ne ya kara cin kwallo ta hudu a ragar City saura minti 11 a tashi daga karawar.

Wannan shi ne karo na biyu da City ta yi rashin nasara a gasar Premier, yayin da West Ham ta fara doke ta 2-1 a Ettihad a makon jiya.