Horo ya ki dambe da Shagon Alabo

Image caption Sarkin Dambe Ashiru Horo daga Arewa

Sarkin dambe Ashiru Horo ya ki ya yi dambe, bayan da shagon Alabo ya bukaci su dambata da safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Makadin 'yan dambe Mamuda Kanoma ne ya hada wasan, bayan da ya yi wa Horo dan damben Arewa kida da kirari, nan take kuma ya wasa Shagon Alabo daga Kudu.

Ba yadda Shagon Alabo bai yi su taka da Horo ba, kai har bangazarsa sai da ya yi, amma Horo ya ce ba zai yi wasan ba, kuma Shagon Alabo ya ce ba shi da abokin dambe da ya wuce Horo kuma saboda shi ya je gidan damben.

Horo ya ce ba zai taka da Shagon Alabo da safe ba, sannan da yammaci ya neme shi ya rasa, yafi kyaunar dan wasan da zai tsaya su taka da safe su kuma kara yi da yammaci.

Shi kuwa shagon Alabo ya ce zai ci gaba da wasa a gidan damben Ali Zuma zuwa lokaci mai tsawo har sai yaga ya doke Horo a gidan.